IQNA

Rubutun kur'ani mafi tsawo da masu ziyarar  Arbaeen suka rubuta a Karbala

15:19 - September 11, 2023
Lambar Labari: 3489796
Karbala (IQNA) Cibiyar Hubbaren Imam Hussain ta gabatar da shirin rubuta kur’ani da aka rubuta da hannu tare da halartar manyan malamai da masu ziyara a taron Arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasa da kasa da ke hubbaren Imam Husain ta gudanar da shirin rubuta kur’ani mai tsarki da hannun maziyarta da suka halarci taron  na Arbaeen.

Wannan shiri dai yana daga cikin ayyuka na wannan cibiya, wanda kuma dimbin malamai da masu ziyara  daga kasashe daban-daban suka halarci shi.

A wata hira da ya yi da shafin gizon hubbaren Imam Hussain, shugaban wannan cibiya Motanzer al-Mansoori ya ce: taron Arbaeen na bana ya shaida muhimman al'amura, daya daga cikinsu shi ne shirin cibiyar mu da kuma goyon bayan makarantar hauza ta kaddamar  a Najaf Ashraf ga maziyarta.

Ya fayyace cewa: An gudanar da wannan shiri ne da taken “Alkawari da Alkur’ani”, wanda ke mayar da martani ga kokarin bata littafin Allah.

Al-Mansoori ya kara da cewa: Wannan shiri ya shaida kyakkyawar mu'amala daga masu ziyara daga kasashen duniya daban-daban (maza da mata) a lokacin gudanar da aikin ziyarar Arbaeen, da kuma gudanar da aikin tablig wanda makarantar Hauza ta bayar da gagarumar gudunmawa ta wannnan fuska.

 

 

نگارش طولانی‌ترین قرآن توسط عتبه حسینی + عکس

نگارش طولانی‌ترین قرآن توسط عتبه حسینی + عکس

نگارش طولانی‌ترین قرآن توسط عتبه حسینی + عکس

نگارش طولانی‌ترین قرآن توسط عتبه حسینی + عکس

نگارش طولانی‌ترین قرآن توسط عتبه حسینی + عکس

 

 

4168087

 

captcha